Skip to content

Ginin rubutun labari tare da Lubna Sufyan – 1

A lokuta mabanbanta, tare da manya da ma marubuta masu tasowa, idan har mun zo tattaunawa akan rubutu, tambayar ba ta wuce ta yadda kowa yake tsare-tsaren shi kafin fara rubutu, kuma a irin tattaunawar nan ne na fuskanci dukkanmu muna da rauni ta wasu ɓangarorin, amma babu abinda neman ƙarin ilimi ba ya amfanarwa. Saboda idan aka tara marubutanmu dukkansu, to kaso mafi rinjaye daga cikinmu ba wai aji muka shiga muka koyi rubutun ba, wayar gari muka yi kwatsam muka tsinci kawunanmu a cikin duniyar rubutun. Sai dai wasu a cikinmu kuma daga baya soyayyar rubutun ta yi mana wata irin shiga da ta sa muka zurfafa wajen bincike da karance-karance da suka shafi rubutu don ganin mun inganta rubutun yadda zai ƙara samun karɓuwa a wajen masu karatu, har ma wata rana mu cimma mafarkanmu akai.

Idan aka zo maganar Adabi gaba ɗayan shi, akwai mutane irin su Jibril Adamu Jibrin Rano da yake matuƙar ƙoƙari wajen kawo muƙalu da suka shafi inganta rubutu, musamman ta ɓangaren Daidaitacciyar Hausa da kuma ƙa’idojin rubutu. Abubuwa guda biyu kenan da nake da matuƙar rauni akan su, shi ya sa zan ba wa duk marubucin da zai bibiyi wannan muƙala da zan fara, da ya duba shafin shi a manhajar Facebook, da kuma wannan link na rubuce-rubucensa a nan Bakandamiya Hikaya, domin ƙaruwa da irin waɗannan muƙalun, saboda ni zan yi magana ne akan nawa hanyoyin da nake bi wajen gina jigo ya zama cikakken littafi. Wato abinda ake kira da ‘Book mapping’ a turance.

1. Jigo

Duk wanda yake bibiyar litattafaina, zai fahimci cewa ina ɗaya daga cikin marubutan da suke son ‘Realistic fiction.’ Wato ƙirƙirarren labari, amma irin labarin da ba ya sauka daga al’adunmu da kuma abinda zai iya faruwa a zahiri. Shi ya sa a duk lokacin da zan nemi jigo, ina fara dubawa ne a kusa da ni, me na gani da ya taɓa zuciyata? Wane labari na ji ya faru, wane abu ne idan na ɗauke shi zai ƙayatar da masu karatu? Aure ko zawarci? Cin amana ko gagarumar soyayya?

Idan ɗaya daga ciki na ce zan ɗauka, an yi rubutu akai ya fi a ƙirga, to ni wanne ɓangare ne zan taɓa da zai bambanta da sauran? Ɓangaren da idan an fara karantawa ba zai gunduri mai karatun ba, ɓangaren da zai riƙe masu karatu daga farkon shi har zuwa ƙarshe.

Idan na samu wannan ɓangaren, to zan gina jigona ne akai, in samu takarda da biro in rubuta jigon.

Misali;

  • Jigo: Zumunci, ɓangaren zumuncin da yake ƙulluwa ba tare da alaƙa ta jini ba.
  • Saƙon da nake son isarwa: Anan ina zurfafa tunani, sai in fito da duk wani saƙo ƙarami ko babba da nake so in isar wa masu karatu, yadda idan na fara rubutun, zan ɗauko wannan takardar in duba in ga shin labarin na tafiya tare da waɗannan saƙonnin ko kuwa akasin hakan.
  • Sai kuma ina raba jigona zuwa gida uku kamar haka;

A. Farko (Kashi na farko)

B. Tsakiya (Kashi na biyu)

C. Ƙarshe (Kashi na uku)

A mahangata, kuma yayin rubutu, kowanne a cikin jigon nan shi ma yana da ɓangarori guda uku kamar haka;

A. Farko

– Farkon kashin farko

– Tsakiyar kashin farko

– Ƙarshen kashin farko

B. Tsakiya

– Farkon kashi na biyu

– Tsakiyar kashi na biyu

– Ƙarshen kashi na biyu

C. Ƙarshe

– Farkon kashi na uku

– Tsakiyar kashi na uku

– Ƙarshen kashi na uku

Idan muka kalli waɗannan rabe-raben na sama, akansu za mu iya gina jigo ta yadda zai tashi har ya zama cikakken littafi. Mene ne zai faru daga farko? Tsakiya da kuma ƙarshe, a farkon labarin, za a fara ne daga tushe? Kan iyaye ko kakannin taurarin, sai a zo kan iyayen, sai kuma a fara hasko taurarin, inda kashi na farko zai ƙare, sai a tsallaka kashi na biyu a ga abubuwan da za su faru, hargitsin da yake cikin labarin, daga farko, tsakiya da kuma ƙarshen hargitsin, sai kuma kashi na ƙarshe inda za’a warware duka ƙullin da yake cikin labarin.

Ina fitar da duk wannan ne saboda lokacin da zaren labarin ya fara ƙwace min sai in ɗauko takardata in duba in ga yadda na tsara abubuwan za su kasance. Don wani lokacin ma bayan na gama yin duk wannan, na kan rarraba shi zuwa shafi-shafi sai in yi tsokaci na kaɗan daga cikin abinda zai faru a shafin, duk da cewa lokuta da dama yanayin tsarin shafukan suna canzawa.

 Wani abin da na yi hasashen zai faru gaba ɗaya a shafin, sai ya ɗauke ni shafuka uku idan na fara faɗaɗawa bai kai ƙarshe ba, amma dai yana taimaka min sosai a duk lokacin da na samu abinda ake kira da “Writer’s block” a turance, na kan duba in gani. Kuma za ku ga daga fara rubutun ma sai wasu abubuwan da ba ka tsara da su ba su dinga zuwa maka, za ka dinga cin karo da gyare-gyaren da ba za a rasa a jigon ba da zai ƙara wa labarinka armashi.

2. Yare da gari

Yare ne abu na biyu da nake dubawa bayan gina jigo, yaren taurarina, Hausawa ne? Fulani ko Barebari? Shin yaruka nawa ne ma nake so a cikin littafin gaba ɗaya. Idan na rubuta su, sai kuma in tsallaka in zaɓi gari. Garin da zan gina labarina a ciki kenan. Birni ne daga farko har ƙarshe? Ko daga ƙauye ne ake dawowa birni, ko kuma duka biyun ne, ƙauye da birni. Idan na gama yanke hukunci, sai in fito da sunan birni, da ƙauyukan. Sannan yaren da na zaɓa, idan Hausawa ne, ‘yan asalin wacce jaha ce? A jahar tasu suke zaune ko kuma wani dalili ya sa sun baro tasu zuwa wata.

Nakan fito da duka waɗannan abubuwan, sai kuma in duba in ga waɗanne abubuwa nake buƙata a waɗannan garuruwan da na zaɓa, na san garin? Na taɓa zuwa? Idan na san garin dole ba zan rasa sanin wasu abubuwa dangane da garin ba, na kan buƙaci abubuwa kamar haka;

  • Sunayen unguwanni, inda masu hali sukafi zama, da kuma akasinsu, a wajen unguwanni ina ƙarawa da duba shekarun da labarina zai ginu akai. Misali daga 1985 ne zuwa 2020, saboda haka ina buƙatar sanin tsofaffin unguwanni da suka wanzu tun daga wancan ƙarnin, da ma sababbi.
  • Makarantu, boko da Islamiyya. Haka suma waɗannan , ina buƙatar wanda suka wanzu daga ƙarnin shekarar ginin labarin.
  • Gidajen cin abinci irin su restaurant.
  • Wuraren shaƙatawa.
  • Sunayen Otal
  • Asibitoci na masu zaman kansu da kuma na gwamnati.

Na kan zurfafa bincike na daga manhajar Google har ma da neman mutane mazauna waɗannan garuruwan don neman ƙarin  haske akan duk wani abu da nake nema. Irin waɗannan binciken duk idan na kammala ina adana su ne ko da zan sake buƙatar amfani da su a gaba. Sannan ta ɓangaren yare, idan misali ina so in yi amfani da Fulatanci a matsayina na Bahaushiya, na kan duba in ga Fulanin wanne gari nake son sakawa, na Adamawa ko Gombe? To sai in zo in yi cigiya har sai na samu ko da mutum ɗaya ne Bafulatani ko Bafulatana mazauna wannan jahar, don in yi musu wasu ‘yan tambayoyi game da al’adunsu da kuma sunayen da zai iya kasancewa zan buƙata a wajen rubutun. Zan kuma roƙi alfarmar sake tuntuɓarsu idan na zo wani mataki a cikin rubutun da zan sake buƙatar neman taimakon su. Wataƙila ina so in ɗan saka magana ne da yaren jefi-jefi, to wannan maganar da taurarina za su faɗa sai in zo in tambayi yadda za a faɗe shi da yaren, ni kuma in je in rubuta.

Kamar yadda na faɗa ne daga farko, ina son ya kasance ban sauka daga kan abinda zai iya faruwa a zahiri ba, shi ya sa tun daga matakin farko zuwa ƙarshe na kan yi iya ƙoƙarina wajen binciko abubuwa irin waɗannan. Misali a ce zan hasko cikin makarantar jami’a, mu ɗauki ABU Zaria misali, to ina so duk wani wanda ya yi jami’ar ya gama, ko yake kan yi ya ji cewa nima ɗin tamkar a nan na yi karatuna, saboda na zayyana abubuwan da suke faruwa a makarantar kamar yadda suke. To idan gari ne ma, ina so ko da ban taɓa zuwa ba, to a cikin masu karatu mazauna garin su ji kamar ni ɗin ma a garin nake zaune saboda yadda na fito da asalin al’adunsu, na yi magana kan makarantun da suke da su, bawai shaci-faɗi ba.

Bincike abune mai matukar muhimmanci a wajen duk wani marubuci, kuma kin yin bincike yana jawo nakasu mai girma ga labari. Shi ne za ka ga misali, ka dauki ma’aikacin wata masana’anta da albashin shi bai wuce dubu hamsin ba, amman yana hidimar wanda yake daukar albashin dubu dari biyar. Amman idan ka yi bincike zaka kaucewa faruwar irin wannan abin, kuma wannan binciken hanya ce ta karin ilimi a gareka dama makaranta gabaki daya. Ya zamana idan kana da ma’aikacin banki mai matakin karatun diploma to ka bincika ka san wanne irin aiki masu wannan matakin suke yi a bankuna, sannan ya yanayin albashinsu yake. Wadannan abubuwan suna matukar karawa labari armashi.

A kashi na gaba za mu yi magana ne akan abinda ake kira “character development” a turance, wato gina su kansu jaruman littafin.

4 thoughts on “Ginin rubutun labari tare da Lubna Sufyan – 1”

  1. Avatar

    Haƙiƙa na ji dadin karanta wanann takaitaccen bayani mai cike da ilimi
    Muna godiya hamshaƙiyar marubuciya, lallai duk wanda yake karanta littafin ki zai ji tamkar a zahiri abin yake faruwa,
    Na karanta wasu daga littafanki, kamar su,
    1:-Mijin Novel *Labarin Gaba ɗaya ya tafi ne akan Aure, wani irin miji ya dace mace ta zaba a yayin budurci! Kyau ba shine yake samar da zaman lafiya aure ba, na ƙaru da abubuwa masu yawa a littafin*,
    2:- RAYUWAR mu *labarin akan zumunci da sauran ƙaddarorin na rayuwa, in akwai haɗin kai da soyayya duk abinda zai faru a family ba zai rushe ta ba, sannan in Allah ya tashi zai iya haɗaka zumunci mai kyau da wadanda baka sani ba, littafin cike yake da zantuka masu taɓa zukata ba tausayi da soyayya mai ban mamaki*,
    3:- Alƙalamin ƙaddara *labarin akan ƙaddarorin rayuwa, yanayi da sauran Al’amuran da ke faruwa a rayuwar yau da kullum na kuskure wasu mutune, labari mai cike da ban mamaki da taɓa zukata, tafiya da hankali mai karatu ban sha’awa*,
    4:- Akan so *Labarin soyayya mai tsafta da BURGEWA, lallai sha’anin iyaye ba karamin al’amari bane, mudum ka saba musu lallai baka ga da kyau ba, labarin kayatar matukar yayi kyau da ban sha’awa*
    Muna godiya sosai✨✨✨🌻

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page