Skip to content

Burin da nake da shi bai wuce na fitar da littafi kasuwa ba – Rabi’atu S. K. Mashi

A ci gaba da tattaunawa da Bakandamiya ke yi da marubuta na wannan zamani, a yau mun yi tattaki mun zaƙulo muku fitacciya kuma shahararriyar marubuciya mai suna Rabi’atu SK Mashi. Marubuciyar ta bayyana irin gwagwarmayar da ta sha game da harkar rubutu, dama sauran abubuwa da suka danganci rayuwarta. Ku kasance damu domin jin ko wace ce Rabi’atu Mashi.

Tambaya: Malama Rabi’a, muna son jin tarihinki a taƙaice idan babu damuwa.

Amsa: Da farko dai sunana Rabi’atu. An haife ni a garin Mashi na jihar Katsina. Na yi primary da secondary duk a cikin garin na Mashi, yanzu haka na tsaya a matakin N.C.E. ne. A bangaren Islamiyya, Alhamdulillahi, dan kuwa  na yi sauka da hardar fiye da rabi na Alkur’ani Mai Girma, ba ni da aure, muna dai fata a gaba. Wannan shi ne takaitaccen tarihina.

Tambaya: Madalla, to ko za mu iya sanin dalilin da ya tsunduma ki a cikin harkar rubutu?

Amsa: Gaskiya yawan karance-karance ne, da kuma sha’awar shi kansa rubutun. Duk lokacin da nake karantu yakan matuƙar burge ni, na ji ina so ni ma na dinga rubutawa ina aika nawa saƙon. Duk lokacin da nake karantu, idan na ga an yi ba yadda nake so ba, sai in ji dama ni ce nake rubutawa da ba zan yi hakan ba. Na kan samu littafi na rubuta nawa ko da a ce zan shekara ban ƙarasa labarin ba.

Tambaya:  To, wane irin ƙalubale kike kai a yanzu, ko kuma kika taɓa fuskanta a rubutunki?

Amsa: Ƙalubalen da na fuskanta dai bai wuce na wani daya taɓa satar mun littafi ba tare da izini na ba, kuma a lokacin da nake kan rubuta shi, abin ya taɓa mini rai sosai. Dan lokacin ba ƙaramar badaƙala aka yi da ni ba, daga ƙarshe ma sai na daina rubuta littafin, na bar masa na ga shin da me zai ƙarasa labarin?

Tambaya: Ko za mu iya sanin zuwa yanzu littatafai nawa kika rubuta kuma wanne ne bakandamiyarki?

 Amsa: Na rubuta littafai za su kai goma sha takwas zuwa ashirin (18 – 20). Bakandamiya ta shi ne Hafsatul Kiram.

Tambaya: Madalla, to ko za mu iya sanin taƙaitaccen labarin bakandamiyar taki?

Amsa: Hafsatul Kiram labari ne akan wata budurwa da aka yiwa auren haɗi da ɗan uwanta mashayi kuma manemin mata. Saboda kyawawan halayenta tare da kyautata zaton za ta iya canja shi. Ta karɓi auren ɗan uwanta hannu bibbiyu saboda biyayyar iyaye, ta sha wahala sosai a hannunsa, ya nuna mata ƙiyayya sosai kafin ta samu nasarar karkato da hankalinsa gare ta da kuma samun soyayyarsa.       

Tambaya: Wane irin buri kike da shi a harkar rubutu?

Amsa: Burin da nake da shi bai wuce na fitar da littafi kasuwa ba, ina nan da wannan burin in sha Allah. Ɓangaren shahara kuma Alhamdulillah duk in da ya kamata na kai na kai, duk da ban yi suna ba sosai, amma dai ina jin dadin yadda aka sanni sanadin rubutuna.     

Tambaya: Shin ki na da wata uwarɗaki ko kuma maigida a harkar rubutu?

Amsa: Gaskiya ba ni da maigida ko uwardaki a ɓangaren rubutu, sai dai mutanen da suke ƙara mun karfin gwiwa ta ɓangaren rubutu, su ne, Abdulazeez (Ililee), Abdul Jega, Najibullahi da kuma Ahmad Funtua.       

Tambaya: To mun ji ko wani marubuci da irin salonsa a harkar rubutun, Malama Rabi’a ke Salon wane marubuci ne ya fi burgeki, har kike ganin zai iya zame miki allon kwaikwayo?

Amsa: Gaskiya salon rubutun Halima K/Mashi yana matukar burgeni sosai. 

Tambaya: A wane yanayi rubutu ya fi yi miki daɗi? 

Amsa: To ba zan iya cewa ba, saboda ni ba ni da keɓaɓɓan lokacin yin rubutu, ina yin sa a ko wane lokaci ya zo mini, cikin dare ne ko da asuba ko da rana, kai ko da cikin mota ne a yayin tafiya ina iyayin rubutu na, shiyasa ba ni iya cewa ga lokaci.

Tambaya: Shin Adabin Hausa ya tasirantu da adabin wani yare? idan e, wanne irin tasiri ya yi? idan kuma bai tasirantu ba me ya sa?

Amsa: Adabin Hausa ya tasirantu da yaren Larabci ne, saboda kalmominmu da yawa suna kamanceceniya da juna. 

Tambaya: Kasancewar rubutun novel da rubutun fim kamar ɗanjuma ne da ɗanjummai shin kina sha’awar rubutun fim? Idan hakane, me ya sa? idan ba haka ba ne, saboda me?

Amsa: Ina da sha’awa sosai, ina so kamar yadda nake rubutawa ana karantawa na rubuta a hau, na zauna ina kallon wasu da yanayin da na tsara musu, kuma suna faɗin kalaman da na rubuta a bakinsu. Kayya! Ba ni tunanin akwai wanda zai ƙi damar nan idan ta zo masa, duk dai Hausawa sun ce shan koko daukar rai.

Tambaya: Wace irin shawara za ki bawa ƙananan marubuta masu tasowa a matsayinki na marubuciya da ta kwana biyu a harkar rubutu.?

Amsa: Su ji tsoron Allah su tsarkake zuciyarsu a kan duk abinda zasu rubuta, su saka wa ransu  za su yi ne domin fadakar da al’umma ko wa’azantarwa da tunatarwa, ba wai don neman suna ko kudi ba. Har ila yau, suke yin bincike sosai kafin su kai ga yin rubutun, sannan su tabbatar suna da jigo mai kyau, kuma su tsara labarin cikin salon da zai ƙayatar. 

Tambaya: Mene ne yake jawo wa ki ga marubuci ya ɗauki rubutu amma ya kasa ƙarasawa, wacce irin shawara za ki bawa irin waɗannan marubutan?

Amsa: Gaskiya sau tari rashin tsara labarin ne daga farko har karshe kafin a fara, da rashin samun kwarin gwiwa daga wurin makaranta, gajiya, da tunanin wani labarin da suke ganin zai fi wancan samun karɓuwa ko za su fi jin dadin rubuta shi.

Tambaya: A duk cikin taurarin labaran da kika rubuta, wanne kika fi so? Kuma me ya sa?

Amsa:  A gaskiya na fi son Hasfatul Kiram saboda labarin ma na rubuta shi ne da halayen da nake fatan mai sunan ta tashi da shi, na haƙuri, taimako da kuma juriya tare da kauda kai.

Tambaya: A wacce ƙungiya kike rubutun, kuma mene ne manufar ƙungiyar taku?

Amsa: Ina ƙungiyar Nagarta Writers Association, manufarmu ita ce kawo gyara da yin rubutu mai tsari da ma’ana, da kuma taimakawa ƙananan marubuta masu tasowa.

Tambaya: Me za ki iya cewa akan lamarin kasuwancin online na littafi?

Amsa: To gaskiya abun ya yi matuƙar burgeni da yadda marubuta ke cin moriyar fasaharsu, kuma abun ya samu karbuwa sosai ga makaranta har ma da marubutan saboda yadda har masu buga littafin suka fara dawo da harƙallarsu online ɗin, wannan ci gaba ne sosai a zamanance ga rubutun.

Tambaya: Kin taɓa siyar da littafi? idan kin siyar wanne ne?

Amsa: A gaskiya ban taɓa siyarwa ba, amma ina saka ran siyarwa a gaba in sha Allah.

Tambaya: Kin ce an taɓa satar miki littafin da kike rubutawa, shin wanne mataki kika ɗauka akan satar da aka yi miki?

Amsa: Ba ni ce na ɗauki mataki ba ƙungiya ce, manyan ƙungiyata sun same shi an yi maganar fahimta sosai kuma ya bada hakuri akan hakan, sai dai ni na gaza ƙarasa musu labarin.

Tambaya: Kun taɓa yin gamayya wajen rubuta littafi ke da wasu? Idan kun taɓa, ya ya sunan littafin?

Amsa: Mun yi gamayyar rubuta littafi da wasu ba mutum ɗaya ba. Mun rubuta Ba Ni Ba Ne ni da Amratu A Mashi, mun rubuta A Yini Ɗaya da wani da na kasa tuna sunansa, mun rubutu Dodon Jatau da suanan RAZ, wato Rabi’atu SK Mashi da Amrah A Mashi da kuma Zahra BB, mun rubuta Masarautarmu har ila yau tare da su, da wani shi ma na manta sunansa. Sai kuma mun rubuta Amanar Aure da Haka So Yake tare da Abdul Jega. Mun rubuta Mafarin So da Duniya Gidan Kashe Ahu tare da Mrs Umar.

Tambaya: Daga ƙarshe, me za ki iya cewa game da Bakandamiya Hikaya?

Amsa: Wani babban ci gaba ne da ya zo wa marubuta da makaranta koma in ce al’umma baki daya, yana taimakawa marubuta tare da basu damarmaki na baje kolin fasaharsu har ma su ci moriyar hakan, ga sauƙi da kuma dadin amfani. Muna godiya tare da fatan wata rana za a dawo mana da Application dinsa, wato manhajar.

An yi hira da Rabiatu SK Mashi a ranar Talata, 15 ga watan Satumba 2020; 9am – 6pm kai tsaye a Taskar Bakandamiya. An kuma tace tare da sabunta hirar a ranar 20 ga watan Satumbar 2023.

Tsara tambayoyi da gabatarwa: Maryam Haruna tare da Hauwa’u Muhammad

Tacewa da sabuntawa: Asma’u Abdallah (Fulani Bingel)

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page