Skip to content

Rubutu dai rubutu ne, babu wanda ya fi wani sai wanda ya iya tsara labari tare da salon isar da sako mai armashi – Danladi Haruna

A yau hirarmu da marubuta ta yi babbar kamu, inda ta yi kacibis da hazikin marubuci, manazarci, kuma akawu, Danladi Haruna. Ga yadda hirar tamu ta kasance.

Tambaya: Da farko dai za mu so jin cikakken sunanka da kuma taƙaitaccen tarihin rayuwarka in ba za ka damu ba.

Amsa: Assalamu Alaikum. Sunana dai Zakariyya Haruna wanda ake wa laƙabi da Ɗanladi. An haife ni ne a jihar Kano, unguwar Gyaɗi-gyaɗi ranar 12 ga Yuli, 1981. Na yi karatun zamani da na Muhammadiyya daidai gwargwado. Ina da matakin ilimi na Masta a fannin gudanar da kasuwanci watau Master of Business Administration. Haka kuma ina da shaidar ƙwarewa ta cikakken akawu watau Associate Chartered Accountant na Ƙungiyar Ƙwararrun Akantoci ta Nijeriya watau Institute of Chartered Accountants of Nigeria (ICAN). Ina da satifiket da dama na ɓangaren rubutu da nazari da na manhajojin kwamfuta da sauransu. Suna da dama waɗannan.

Tambaya: Madalla, Tun yaushe ka fara rubutu? Kuma mene ya ja hankalinka har ka fara rubutun?

Amsa: Rubutu na jima ina taɓawa. Tun lokacin muna firamare kasancewa ta mai son karatu da sauraron rediyo, da sauran labarun almara da na hikayoyi da sauransu. Haka dai sannu a hankali har mai karatu ya rikiɗe zuwa marubuci. Kodayake, rubutun da nake ganin na saka ni a gwadaben marubuci, shi ne wani littafi da na rubutu mai suna Furar Danƙo a shekara ta 2002. Daga kansa kuwa na ci gaba da rubutu iri daban-daban.

Tambaya: Wanne irin matsaloli ka fuskanta a harkar rubutu, kuma ta wacce hanya ka bi har ka tsallake?

Amsa: Yawancin rubuce-rubucena ina yin su bisa son rai ne. Wani lokaci yana iya zama tamkar bahaya. Idan ya taso wajibi ne a fitar da shi. Kuma ka san cewar aikin sa kai ya fi bauta ciwo. Don haka, koda akwai wasu matsalolin akan rufe ido yi abin da ya dace. To amma yawancin matsalolin marubuta sun haɗa da rashin lokacin aiwatar da bincike, da rashin goyon bayan wasu daga al’umma da kuma matsalar kasuwa. Wanda idan marubuci don samun kasuwa yake a halin yanzu, to sai dai ya ɗora hannu a ka kurum. Muna fatan samun warwarewar matsalolin da suka baibaye marubuta nan ba da jimawa ba.

Marubuci Danladi Haruna

Tambaya: Zuwa yanzu littattafai nawa ka rubuta? Kuma za mu so mu ji sunayensu.

Amsa: Ni Kusan kullum ina rubutu. Ina rubuta labarin ƙirƙira a intanet. Sai dai littatafan da na rubuta cikakku duka – duka goma 10 ne. Daga ciki an wallafa guda 3 rak, watau Saura Ƙiris, Tekun Labarai da kuma Ɓarayin Zamani. Ana samun Tekun Labarai a shafukan sayar da littattafai na Okada da na Konga da nan Bakandamiya. Shi kuwa Ɓarayin Zamani ana iya samunsa kyauta a gidan archive.org. Na sake shi kyauta ne saboda jama’a su karanta su ƙaru da ilimin sanin hanyoyin kare kansu daga maha’intan da ke cutar mutane ta intanet. Kuma Alhamdulillahi kwalliya ta biya kuɗin sabulu.

Tambaya: Wanne littafi ka fi so a duk cikin littattafan da ka rubuta, kuma me ya sa?

Amsa: Littattafai na duka ina sonsu amma wanda na fi jin dadin karanta shi da kaina shi ne Ɓarayin Zamani, saboda abubuwan da na ambata a ciki waɗanda suka shafi harkar kwamfuta da intanet da kuma kare kai daga masu satar zamani ta waya ko ta intanet. Littafin na da amfani ba wai domin nishaɗi ba kawai, har ma da yadda za ka fahimci ‘yan damfarar intanet da yadda za ka kare kanka. Sau tari idan ina karanta shi sai na yi ta mamakin irin abubuwan da ya ƙunsa kamar ba ni ne na rubuta shi ba.

Tambaya: Wanne littafi ne da ka taɓa karantawa kuma ya fi burge ka?

Amsa: Na Hausa dai har yau Magana Jari Ce ba na gajiya da karanta ta. A na Ingilishi kuma suna da yawa kamar littafan James Brown ko na Sydney Sheldom musamman Digital Fortress da Sky Is Falling da sauransu. Littattafan nazari kuwa ba a gajiya da su na Hausa ko na Ingilishi.

Tambaya: Idan za ka yi rubutu, shin ka kan tsara komai da komai ne kafin ka fara ko kuwa kai tsaye kake farawa?

Amsa: Kamar yadda na faɗa a baya, ina tsara dukkan rubutun da zan yi daki-daki ta hanyar synopsis sannan na yi block. Sai kuma na fitar da hawa da gangara da sauka da tsalle da tashi duka. Sau tari ina ɗora rubutuna akan doran nan da ake kira story line ko story act da sauransu. Duk da haka wani labarin na iya zuwa lokaci guda na rubuta shi. Daga nan kuma ba zan kara tunawa da shi sai na waiwaye shi.

Tambaya: Ya kake yi idan wani tunani sabo ya zo maka game da wani rubutu na daban alhalin kana tsakiyar rubuta wani. Ka kan saki wancan ne ka yi wannan sabon ko kuma sai ka gama da wanda ka fara?

Amsa: Ina iya haɗa labarai biyu ko fiye ma a lokaci guda ina rubuta su musamman gajerun labarai. Wani lokaci ma garin ƙoƙarin rubuta wani sai ka ga fikirar wani ta samu. Don haka kurum da zarar na ji fikirar ta zo, sai shi ma na aza harsashin rubuta shi. Wani zubin ma, labarin da na tuno daga karshe nake fara kammalawa kafin na kammala wanda na fara tun farko.

Tambaya: Ma sha Allah! Wanne littafi ne ya fi ba ka wahala daga cikin dukkan litattafan da ka taɓa rubutawa?

Amsa: Littafin Hanyar Jidda na soma rubuta shi tun 2008 har yau ban gama ba. Kuma labarin duka yana kaina. Na yi masa dukkan abin da nake yi wa labari amma har yau na gagara kammala shi. Sai dai ina jin dadin rubutunsa duk lokacin da na waiwaye shi. Saboda ta dalilin rubutun littafin na san hanyoyin zuwa Kamaru da Chadi da Sudan har zuwa Bar Sudan gefen Bahar Maliya. A bi ta Kasala a isa Bar Sudan a haura bahar Maliya a je Jeddah ko Yemen. Na rike sunayen hanyoyi da dama duk da ban taɓa zuwa nan haka ba. Ta dalilin littafin na tattauna da mazauna ƙasashen nan da yawa musamman Hausawan Chadi da na Sudan da wasu ƙalilan da ke Yemen da Saudiyya. Ina fatan dai na iya kammala shi da wuri kafin labarin ya gudu daga kaina.

Tambaya: Wani lokaci kan marubuci kan cushe har ya kasa rubuta komai. Shin ka taɓa shiga irin wannan yanayin? Kuma ta wace hanya ka bi wurin magance hakan?

Amsa: Tabbas hakan na faruwa sau da dama kuwa. Na taɓa halartar wani kwas dangane da dabarun rubutu. Ɗaya daga cikin abubuwan da na ji daɗin kwas ɗin shi ne dabarun da aka koya mana lokacin da kana cikin rubutu sai ka ji ɗif basirar ta ƙare. Ka kakare. Babu gaba babu baya. Hanyoyin su ne, tun farko marubuci ya tsara abubuwan da zai yi mataki mataki watau synopsis. Sannan ya karkasa synopsis ɗin nasa zuwa ɓangarori. Kullum da abin da zai ɗauka ya rubuta har ya ƙare. Sannan a ware lokacin yin bincike da nazari da tambayoyi ga inda ya dace. Idan kana rubutu, sai ka ji basirar ta ƙare, sai ka ajiye da zummar sake waiwayarsa. Ko ka tashi ka kama wani aikin, ko ma ka yi barci abinka. Da zarar ƙwaƙwalwarka ta huta, za ka ji basirar ta dawo. Amfanin yin gajerun rubutu ana ajiyewa watau blocking yana da yawa. Wani lokacin idan kana rubutu ka kakare, kana duba synopsis dinka ko blocking ɗinka nan da nan sai ka tuna ka ci gaba.

Tambaya: Madalla, yanzu lokaci ya canza, haka zalika al’amura da dama na mutane su ma sun canza wanda na wasu yake zuwa a karkace, har ta kai ga yanzu rubutun littafin batsa abun so ne ga wasu mutanen. Shin wane kira za ka yi wa irin waɗannan marubuta?

Amsa: Kamar yadda na faɗa a baya, rubutu na zuwa ne gwargwadon wayewa da shekarun marubuci. Tun wuri ya kamata marubuci ya yiwa kansa faɗa, ya rubuta abu mai ma’ana da ko ina aka tsayar da shi zai iya karantawa ba tare da taradaddi ba. Masu rubutun batsa da suke ganin burgewa ce ko wayewa, ba za su fahimci illar abin ba sai lokacin da ruwa ya karewa ɗan kada. Kuma ma ni gani nake yi marubutan batsa basu da wata fasaha illa irin abin nan na kiɗanki na jiyo. Da za a bibiyi rubutun kusan duka abu ɗaya ne a cikinsa. Babu wani abu sai yaudarar kai da ɓata lokaci.

Tambaya: Ka samu nasarori da dama duba da irin littafan da kake yi irin waɗanda mutane ba sa gajiya da karantawa ne, kuma suna daga cikin waɗanda suka yi suna, kusan duk mai karatun litattafai na Hausa ya san su. Shin waɗanne irin nasarori ne ka samu wajen rubutunka?

Amsa: Nasarorin suna da ɗumbin yawa da gaske. Rubutu ya sa na san mutane da yawa ciki da wajen ƙasar nan. Haka nan na shiga gasar rubutu da yawa. Na yi nasara a cikinsu da dama. Aƙalla na shiga gasanni da suka kai 10 kuma na yi fice a mafi yawancinsu. Misali, gasar Duniyar Marubuta a 2013. Na yi na ɗaya a ɓangaren Wasan Kwaikwayo. Gasar Gusau Institute na yi na biyu a 2018. Gasar Pleasant Library na yi na uku a 2020, da sauransu. Na samu kyaututtuka da dama ta silar rubutu. Sannan ina aiki da mutane da dama duk albarkacin rubutu.

Tambaya: A harkar rubuce-rubuce, waɗanne marubuta ne gwanayenka, da kake koyi da rubutunsu?

Amsa: A rubutu suna da dama. Kusan duk wanda na karanta littafinsa ko wani rubutu nasa, na kan ɗosani wani abu daga gare shi yadda zan kattaba nawa idan buƙatar hakan ta taso. To amma manya daga ciki sun haɗa da Farfesa Ibrahim Malumfashi, da Farfesa Yusuf Adamu da Bala Anas Babinlata da Ado Ahmad Gidan Dabino da Nazir Adam Salihi da Maimuna Idris Beli da kuma Rahama Abdulmajid. A fannin waƙa da wasan kwaikwayo kuwa, Malam Nasiru G. Ahmad shi ne alƙibla ta. Haka kuma, na kan yawaita aika masa rubuce-rubucena yana mini gyara musamman ta fuskar salo da sarrafa harshe da kuma ƙa’idojin rubutu. Shi kuwa marigayi Abubakar Imam, na ɗauke shi wata alƙibla da nake waiwaya duk lokacin da zan yi rubutun gajeren labari. Misali, Tekun Labarai na ari wani salo daga Magana Jari Ce wajen ƙulla gajerun labaru cikin uwar labari ta yadda mai karatu zai yi ta shiga da fita cikin labarai ba tare da an ƙarƙare wanda aka fara tun farko ba.

Tambaya: Ma sha Allah! Kasancewar rubutun novel da rubutun fim kamar ɗanjuma ne da ɗanjummai shin kana sha’awar rubutun fim? idan hakane me ya sa? idan ba haka ba ne saboda me?

Amsa: To, shi rubutun fim musamman wanda ba naka ba. Ma’ana, kai ne marubucin kuma kai ne Furodusa kamar yadda Ado Gidan Dabino MON ya yi a Daƙiƙa Talatin. In dai ba haka ba, to wajibi ne ka sadaukar da lokacinka kacokam domin biya wa daraktoci da furodusoshi buƙatunsu. A halin yanzu ni ba ni da cikakken lokacin rubuta fim musamman irin gaggawar da ake yi da azazazzalar masu rubutun da su yi su gama da gaggawa.

Kada ka manta. Ina aikin akawu, wanda shi ma yana jan lokaci, ga kuma aikin harhaɗa manhajar kwanfuta watau ‘programming’.

Duk da haka, wasu na zuwa wajena neman shawarwari ko gyara a wasu rubuce-rubucen na fim. Na kan bayar da gwargwadon gudummuwar da ta dace idan an buƙaci haka.

Tambaya: Mene ne babban burinka dangane da rubutu?

Amsa: Ina da buri mai girma dangane da rubutu musamman cikin harshen Hausa. Ina fatan rubutun Hausa ya zama ya mamaye duniya ta kafafen intanet. Ya zamana an samar da manyan dandamalai kamar su Amazon KDP da su Watpad da Webnovel da sauransu.

Kuma Alhamdulillahi, ya zuwa yanzu akwai yunƙuri a ciki da wajen ƙasar Hausa dangane da wannan manufa. Ni kaina ina daga cikin wasu tafiyoyin da ake wannan shirin. Ɗaya daga ciki kuwa, wata babbar ƙungiya ce da ke ƙoƙarin zamanantar da harsunan Afrika. Sun ɗauki Hausa da Siwahili da kuma Zulu a matsayin waɗanda za a fara da su.

Aikin da ake yi yanzu haka, sun ce zai ɗauki kimanin shekara guda ana yi. Ina fatan yadda aka fara da ni za a kammala da ni cikin nasara

Tambaya: A naka ra’ayin, tsakanin rubutun online da bugun littafi na hannu wanne ya fi ma’ana da tsari?

Amsa: Hanyar isar da saƙon rubutu ko littafi na da yawa. A da can ana saka marubuci ne a gaba, ya buɗe ya yi ta karantawa mutane. Aka samu lokacin da ake ɗaukar nauyin buga masa littafin ana sayarwa, shi kuma ana ba shi kamasho watau royalty. Da tafiya ta tafi, sai marubutan suka riƙa buga littatafan da kansu a cikin samfurin ɗauki sandarka. Wannan ta samar da ambaliyar marubuta har ake wa rubutun take da Adabin Kasuwar Kano. Sannu a hankali kuma aka samu gidajen rediyo na karanta labaran ga ɗumbin masu sauraro. Sai kuma yanzu da ake sakin rubutun a intanet walau kyauta ko da kuɗi. Su ake kira marubuta online. A nawa ra’ayin, babu wanda ya fi wani martaba ko daraja ko ɗaukaka a tsakanin masu wallafa littafi a Adabin Kasuwar Kano da masu saki online. Wanda ya fi wani kurum shi ne wanda rubutunsa yake da inganci wajen kyautata rubutu da gamsassun bayanai da kuma kwarewa a salo. A dukkan waɗannan ɓangarori akwai kwararru akwai ‘yan dagaji. Akwai haziƙai akwai ‘yan kwamacala. Don haka rubutu dai rubutu ne, babu wanda ya fi wani sai wanda ya iya tsara labari tare da salon isar da saƙo mai armashi.

Tambaya: Wasu mutanen suna tunanin cewa babu abin da rubutu yake jawowa sai ɓata tarbiyya. Shin wacce shawara yakamata a dinga ba irin waɗan nan mutanen?

Amsa: Kowanne rubutu ya danganta da irin manufar marubucin da kuma al’ummar da ya samu kansa tare da waɗanda yake rubutun domin su. Kenan za mu iya cewa rubutu a karan kansa ba ya ɓata tarbiyya sai dai idan marubucin ne lalatacce ya gamu da makaranta ‘yan amshin shata. An samu za ni ta tarar da mu je mu. Sai a yi ta yi. Marubuta da dama suna rubutu ne gwargwadon zarafin shekarunsu, a lokacin da marubuci ke tashen ƙuruciya mafi yawa rubuce rubucensa akan soyayya da rayuwa da holewa da nishaɗi ne da kuma rigima da zungurin sama da kara. Yayin da shekarun hankali suka hau shi yana iya canja akalar rubutunsa zuwa nazarin rayuwa da faɗi tashi da kiri da muzu da sauransu.

Makaranta su ne alkalai, idan sun ga rubutun na cike da batsa da lalata da sakin baki, nan take za su iya bijirewa ko waye su tilasta masa yin ritaya matuƙar ba zai gyara ba. Idan kuma ba a iya samun haka ba, ba zai zama adalci a ce wake ɗaya na ɓata gari ba.

Tambaya: Shin ya kake ganin tafiyar Adabin Hausa? Ma’ana, irin ci gaban da aka samu game da shi a yanzu?

Amsa: Adabin Hausa na samun cigaba amma galibi irin na mai haƙar rijiya ne. Ana samun ƙaruwar marubuta da makaranta amma yawanci daɓen kwalo ake yi. Ka ga rubutu a cukurkuɗe kamar ana cakuɗa ɗan wake. Rubutu babu ma’ana babu waƙafi babu aya. Kuma wai marubuci ne. A da gwamnati na taimakawa harkar adabi da yaren Hausa, amma yanzu kusan ci da ƙarfi ake yi. A wasu makarantun sakandare ɗin ma an daina koyar da Hausa wai saboda ci baya ne. Kenan ba za a iya samun ingantaccen rubutun Hausa ba tunda a kasuwa ake tsinta. A wajen batun bunƙasar harshen babu laifi, domin kuwa har ana ta samun kafafen yaɗa labarai na gargajiya da na zamani, na intanet da na satilayit suna ta yaɗa shi sosai da gaske. Amma ta fuskar rubutu kuwa, babu wani abin yabawa saboda hatta gidajen jaridu yawanci suna tafka kura-kurai a rubutun nasu.

Tambaya: Wacce Karin Magana ka fi so? Kuma me ya sa?

Amsa: Na fi son karin magana mai ɗauke da azanci ko haibaici ko gugar zana. Saboda irin waɗannan sun fi daɗin isar da saƙo yayin da ake son a yi nuni cikin nishaɗi. Misali karin magana irin su, makaho bai san ana ganinsa ba, sai ya ji an zungure shi, Mu gani A kasa, an ce da kare ana biki a gidansu, na munafukinka tabarmarka, zancen banza, zakara ya taka wuka da dai sauransu.

Tambaya: Shin ko akwai wani labarin da ka ke rubutawa a yanzu haka da masoyanka za su yi tsumayin fitowarsa?

Amsa: Littatafin Tekun Labarai na uku da na huɗu nake son fitarwa ba da jimawa ba. Tuni na ƙulla zaruruwan labaran na kuma samar musu da take. Abin da ya rage kurum shi ne samun zama na rubuta su yadda ya dace. Waɗannan littatafai, ci gaban gajerun labaran Littafi na ɗaya da biyu ne. Kowanne littafi akwai irin salon da ke cikinsa. Littafi na ɗaya ɗan sarki ne ke ba wa Sarki labari, littafi na biyu Waziran Sarki ne ke ba wa Sarki. Littafi na uku kuwa mutanen gari ne ke ba wa Sarki labari. Littafi na huɗu kuma mutanen gari ne ke ba wa junansu labari.

Bayan Tekun Labarai na uku da huɗu kuma akwai wani littafi mai suna Hanyar Jidda. Labari ne akan wata ƙirƙirarriyar tafiya daga tashar motar Unguwa Uku zuwa Jidda da ke Saudi Arabiya wadda tauraron labarin ya yi cikin shekaru takwas. Labarin na ƙunshe da abubuwan mamaki da tarihi da al’adu da soyayya da sauransu. Na rubuta labarin ne a bisa abin da ya faru a Sudan a shekarar 2006 tsakanin gwamnatin Sudan da ‘yan Janjawid a yankin Darfur. In sha Allahu ba da jimawa ba za su fito.

Tambaya: Wacce irin shawara za ka iya ba wa sabbin marubuta masu tasowa?

Amsa: Duk wanda zai yi rubutu ya tabbata ya ɗaura aniya ta ƙwarai a ransa ba domin ganin kitson wance ba. A yi rubutu mai tsabta da ma’ana, ba rubutun tir da shiririta ba. A guji rubutun ɓatanci ko batsa da cin zarafin juna. Abu ne mai amfani marubuta su riƙa ba wa junansu labaran da suka rubuta suna yi wa

kansu gyara. Wannan shi ne hadafin da ƙungiyar ANA take kai kuma ta wannan hanyar an yi wa marubuta da yawa gyara mai ma’ana kuma sun amfana sosai ciki kuwa har da ni. Duk mai sha’awar soma rubutu ya yi azama da gaske kuma ya kyautata niyya tare da zurfafa bincike. A guji rubutu mai salon daga buhu sai tukunya saboda gudun butaci.

Tambaya: Ko kana da wani kira ga gwamnati da marubuta ‘yan uwanka da kuma al’umma masu karanta littattafanka?

Amsa: Kira ga gwamnatoci shi ne, kada a manta mafari. Marubuta su ne mafarin cigaban adabi. Yadda ake yi musu shakulatin ɓangaro a wannan lokaci daidai yake da an ci moriyar ganga an jefar da kwaurenta. Ya kamata a ɓullo da sababbin hanyoyin ƙarfafa gwiwar marubuta yadda hazaƙarsu za ta cigaba da kaifafa su riƙa zaƙulo hanyoyin da za a warware matsalolin Arewaci da ma ƙasar Nijeriya baki ɗaya. Haka kuma gwamnatoci na iya kai wa marubuta ɗauki wajen tallafa musu da duk abin da ya dace domin su wallafa rubuce-rubucensu kuma su ci riba. Ba kamar yanzu ba da marubuta ke ta faɗi tashi suna aiki kan jiki kan ƙarfi amma haƙa ya kasa cimma ruwa ta fuskar kasuwancilittattafanka Marubuta ‘yanuwana kuwa, haɗin kai wajibi ne. Haɗin kai shi ne tushen nasara da isuwa ga biyan buƙata. Manyan marubuta su ci gaba da haƙurin tarbiyyantar da mu ƙanana ta hanyar shawarwarin da ƙarfafa gwiwa. Mu kuwa ƙananan marubuta, wajibi ne mu kasance masu ladabi da biyayya da girmama na gaba. Ta haka ne burin da muke da shi na sauya alƙiblar rubutu zuwa na zamani zai kai ga gaci.

Tambaya: Daga ƙarshe, me za ka iya cewa game da Bakandamiya Hikaya?

Amsa: Bakandamiya gida ne kuma zaure ne mai hidima ƙwarai ga harshen Hausa da Adabi. Zan iya cewa babu wani dandalin intanet da yake tiri-tiri da marubutan Hausa kamar sa. Abubuwan da na sani ya yi wa marubuta ba za su ƙidayu ba, musamman fa aka shirya bita ga marubuta domin sanin dabarun rubutun shiga gasa. Kuma daga waɗanda suka bibiyi shirin an samu wadda ta yi nasara da kuma waɗanda labarunsu suka samu jinjina musamman a gasar BBC ta marubuta mata. Haka kuma Bakandamiya ta shirya gasa ta musamman ga kungiyoyin marubuta da aka shafe watanni ana fafatawa daga karshe aka shirya wani gagarumin biki aka karrama ƙungiyoyin da suka yi nasara. Ga kuma hidimar da ake yi wa marubuta wajen tallata su gami da ayyukansu. Babu abin da za mu ce sai godiya da fatan Allah ya ɗaukaki wannan kamfani ya sa ya zama tambari a duk duniya a ji ɗuriyarsa. Amin summa amin.

Tsarawa da gabatarwa: Asma’u Abdallah (Fulani Bingel)

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page